• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GARGADI KAWAI MU KA TURAWA GIDAN TALABIJIN NA CHANNELS BA RUFE SHI MU KA YI BA- NBC

Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya NBC ta ce ba rufe gidan talabijin na channels ta yi ba don zantawa da ya yi da wani kwamandan ‘yan awaren Biafra na IPOB da ke karkashin madugun ‘yan awaren Nnamdi Kanu.

A karin bayanin da NBC ta yi ta ce gargadin channels ta yi ya guji irin wannan zantawa mai cike da miygun maganganu da neman tada fitina daga kungiyar da kotu ta haramta.

NBC ta ce irin wannan takarda a kan aikata kafar labaru idan ta saba ka’ida sannan in an aika takarda ta biyu to mataki ne ya kan biyo baya na tara ko dakatar da lasisin kafar labaru.

A shekarun baya an taba rufe gidan talabijin na channles don samun sa da laifin saba ka’idar lasisin da hukumar NBC ta ba shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “GARGADI KAWAI MU KA TURAWA GIDAN TALABIJIN NA CHANNELS BA RUFE SHI MU KA YI BA- NBC”
  1. Excellent weblog here! Additionally your web site a lot up fast!
    What host are you the use of? Can I am getting your affiliate link
    to your host? I wish my site loaded up as fast
    as yours lol

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *