• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GANGAR FETUR NA DADA DARAJA A KASUWAR DUNIYA INDA TA HAURA DALA 67

Gangar danyen man fetur na kara daraja a kasuwar duniya inda a zango uku a jere ta ke kara daraja.

A yanzu dai farashin gangar danyen fetur ya kai dala 67.20 da hakan ke nunu zai iya kara daraja.

Kungiyar kasashe masu arzikin fetur ta duniya OPEC za ta duba rage hako man a watan gobe yayin da ta ke shirin taro a ranar 28 ga watan nan.

Kazalika karin farashin na nuna kyautatuwar arzikin manyan kasashen masana’antu na duniyar Amurka da Sin.

Takunkumin da Amurka ta sanya kan Rasha na lamuran cinikaiyar fetur don zargin tsoma baki ga lamuran zaben ta, ba zai shafi darajar farashin fetur din ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *