• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GABAR KABILANCI TA HADDASA ASARAR RAYUKA A KUDANCIN GOMBE

Gabar kabilanci a yankin kudancin Gombe ta haddasa arangama tsakanin kabilu biyu inda a ka samu asarar rayuka. Akalla mutum 15 sun rasa ran su.

Fitinar ta auku ne a wasu kauyuka Nyuwar da Jessu a yankin karamar hukumar Balanga inda hakan ya haddasa zubar da jini.

Wannan lamari ya shafi kabilar Lunguda da Waja da ke zaune a garuruwa da ke makwabtaka da juna.

Tuni gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ya aiyana dokar hana yawo a yankunan da lamarin ya shafa don dawo da doka da oda.

Kazalika gwamnan ya yi alwashin cafko wadanda su ka haddasa tashin fitinar don fuskantar hukunci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.