• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GABANIN RANAR DIMOKRADIYYA BATUN KARBA-KARBA DA SALON SHUGABANCI YA TASO

Intro-Gabanin bukin ranar dimokradiyya ta bana a Najeriya a asabar din nan, batun mulkin karba-karba da salon shugabanci ya taso.

In za a tuna shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauya ranar daga 29 ga mayu zuwa 12 ga yuni don karrama zaben Moshood Abiola da soja su ka soke a 1993…..

Manyan jam’iyyu APC da PDP ne su ke tsaka mai wuya na wannan tsari na ba da takarsr karba-karba tsakanin arewa da kudu bayan nasarar wa’adin shugaban kasa sau biyu na shekaru 8.

PDP ta samu nasarar bin wannan salo bayan kammala mulkin Obasanjo a 2007 inda mulkin ya dawo hannun marigayi shugaba Umaru ‘Yar’adua na arewa, yanzu kallo ya koma kan APC a 2023 don wasu jigogin ta na da ra’ayin a bar batun karba-karba a koma cancanta.

Wannan ya sa wasu ‘yan jam’iyyar irin Barista Bello Mustapha ke cewa su na gwagwarmayar ganin an mutunta tsarin na karba-karba duk da ba ya tsarin mulkin kasa.

A gefe guda kuma kan salon shugabancin wuka da nama hannun mutum daya;  wasu ‘yan siyasar na cewa mulkin shugaba mai cikekken iko da Najeriya ke amfani da shi shigen na Amurka na da tsada da jidali.

Tsohon minista Barista Solomon Dalung na ba da shawarar sauya salon zuwa na firaminista salon na Burtaniya.

Kwanan nan shugaba Buhari ya tabbatar da shirin sa na sauka daga mulki da zarar wa’adin sa ya cika ta hanyar kaucewa neman tazarce karo na uku.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.