• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FUROFAGANDA BOKO HARAM TA YI KAN KAKKABO JIRGIN MU-SOJAN SAMAN NAJERIYA

ByNoblen

Apr 4, 2021

Rundunar sojan saman Najeriya ta ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun yi furofaganda kan daukar alhakin hatsarin jirgin yakin rundunar a jihar Borno.

In za a tuna ‘yan ta’addan sun nuna yanda su ka harbo jirgi ya na fadowa daga sama da nuna gawar wani soja a kasa.

Rundunar dai ba ta karyata cewa jirgin ya yi hatsari ba, amma ta ce ba Boko Hatam ta harbo jirgin ba.

Rundunar ta ce a yanda a ka nuna jirgin ya kama wuta daga sama bai dace kuma a gan shi a gu daya a hade ba. 

A bayanan rundunar, alamu na nuna ‘yan Boko Haram sun harhada hotuna ne don yada furofaganda.

Tuni rundunar ta baiyana sunayen matukan jirgin biyu da ya yi hatsari da su ka hada da John Abolarinwa da Ebiakpo Chapele.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *