• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIYE DA ‘YAN HOUTHI 190 A KA KASHE A MARIB CIKIN SA’O’I 24 DA SU KA WUCE

ByNoblen

Dec 12, 2021 , ,

Rundunar gamaiyar larabawa ta tabbatar da cewa fiye da ‘yan tawayen houthi 190 a ka hallaka a tsawon sa’a 24 a yankin Marib na kasar Yaman.
‘Yan tawayen dai da ke samun goyon bayan Iran na cigaba da cijewa wajen neman kwace yankin Marib daga gwamnatin kasar ta Abed Rabbo.
Rundunar ta kai farmaki 26 kan ‘yan tawayen da hakan kazalika ya ragargaza motocin yaki 20 da bigiren harba jirage marar matuka.
Yankin Mariba mai arzikin iskar gas ne kadai ya rage a hannun zababbiyar gwamnatin ta Abed Rabbo a arewacin kasar Yaman.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.