• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIYE DA PALASDINAWA 100 SU KA RASA RAN SU A SANADIYYAR HARE-HAREN ISRAILA

Zuwa yanzu fiye da Palasdinawa 100 ne su ka mutu a sanadiyyar hare-haren da sojojin Israila su ke kai wa kan yankunan Palasdinawa musamman Gaza.

Wannan ya biyo bayan fitinar da ta tashi a takaita shiga ko walwalar Palasdinawa a masallacin Kudus.

Kwana hudu kenan a jere Israila na barin wuta kan Gaza inda a yanzu ma ta fara tara tankunan yaki a kan iyaka.

Cukin adadin wadanda su ka mutu 27 yara ne kanana na Palasdinawa.

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce harin ba zai kawo karshe nan take ba don yanda Yahudawa ke fatan za a rugurguza shugabannin Hamas a yankin na Gaza.

Palasdinawa na cigaba da kai harin ramuwar gaiya ta hanyar cilla rokoki da hakan ke karamin tasiri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.