A kasa da wuni daya, mutum dubu 450 ne su ka yi rejistar aikin hajjin bana a cikin Saudiyya biyo bayan bude shafin yanar gizo na rejistar.
Cikin wadanda su ka nemi damar kashi 60% maza ne kashi 40% mata.
Gaba daya mutum dubu 60 za a ba wa dama su gudanar da hajjin kuma a iya cikin Saudiyya kadai don an dakatar da shigowar alhazai daga ketare shekara biyu a jere don fargabar yaduwar korona bairos.
Ma’aikatar aikin hajji ta Saudiyya ta ce ba za a yi la’akari da wanda ya yi rejista da wuri ko ya yi jinkiri ba wajen zabar wadanda za su gudanar da aikin hajjin.
Hakanan za a bar shafin a bude har zuwa ranar 23 ga watan nan.
Kazalika ba za a bar yara kasa da shekaru 18 su shiga aikin ba, hakanan za a fi ba da dama ga wadanda su ka haura shekaru 50 a duniya wadanda ba su taba samun damar aikin ba.