• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIYE DA KASHI 60% NA ‘YAN LEBANON SUN AUKA TALAUCI

ByNoblen

Jul 7, 2021 ,

Alkaluma na nuna fiye da kashi 60% na ‘yan Lebanon sun auka talauci bisa mizanin talauci na duniya wato samun kasa da dala daya a wuni.

Firaministan rikwan kwarya na kasar Hassan Diab ya ce ‘yan kwanaki kailian su ka rage kasar ta daidaice matukar ba a kawo mu su dayki ba.

Tun fashewar boma-boman tashar teku a babban birnin kasar Beirut a bara inda fiye da mutum 200 su ka mutu, kasar ke cikin matsaloli da kunci.

Kudin kasar ya rasa darajar fiye da kashi 91%.

A jawabi da a ka yada a talabijin Diab, ya bukaci taimakon kasashen da ke hulda da kasar ya na mai cewa neman taimakon ba laifi ba ne don in kasar ta fada mummunan yanayin to zai iya shafar wasu kasashen ketare.

Har yanzu tsohon firaministan kasar Sa’ad Hariri da ya samu kuri’un sake dawowa firaminista ya kasa kafa gwamnati don halin da kasar ke ciki da rashin jituwar sa da shugaban kasar Michel Aoun.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *