• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FITINAR FILATO-AN TURA DIG LEMU YA JAGORANCI TAWAGAR BINCIKE

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali ya tura tawagar zaratan jami’an rundunar don gudanar da bincike kan kisan gilla ga matafiya a Jos jihar Filato.

Tawagar na karkashin mukaddashin sa mai kula da jihohin arewa ta tsakiya DIG Sanusi Lemu.

Jami’an za su bincika yanda lamarin akasin ya faru da karfafawa jama’a guiwa cewa rundunar na nan wajen kula da kare rayukan su.

Zuwa yanzu rundunar ta ce an cafke mutum 20 da a ke tuhuma da kashe matafiyan da su ka taso daga zikirin jumma’a a Bauchi kan hanyar su ta komawa gida.

Kazalika an ceto mutum 33 baya ga jana’izar kimanin mutum 30.

Babban sufeton ya bukaci jama’a su ba wa rundunar goyon baya don tabbatar da bin doka da oda.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.