• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FITINA A FILATO-MUTUM 17 SUN RASA RAN SU

Rundunar ‘yan sanda a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutum 17 da kuma kona gidaje 85 a fitina a yankin Bassa da Riyom.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN ya ruwaito kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edward Egbuka ya baiyana haka ga manema labaru bayan taron lamuran tsaro na jihar a gidan gwamnati a Jos.

Egbuka ya ce gwamnan jihar Simon Lalong ya yi gargadi ga masu son tada fitina cewa za a dau mataki a kan su.

Filato na fama da kalubalen ramuwar gaiya da kan sa kamar rikici ya kwanta sai a wayi gari wasu sun kai hari mai muni.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *