• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRST BANK: MUN MIKA WUYA GA HUKUNCIN BABBAN BANKI

BySafina Sadisu Mahmoud

May 1, 2021

Bankin First bank da ke cikin manyan bankunan Najeriya ya ce ya mika wuya ga matakin korar shugabannin gudanarwa na bakin da babban bankin Najeriya CBN ya yi.

In za a tuna bankin First ya kwabe shugaban bankin Sola Adeduntan inda ya nada Gbenga Shobo.

Yanzu dai bankin na First na kokarin nuna ya na biyayya ne ga duk umurnin babban bankin, kuma matakin sauyawa da sake rusawa bai shafi hada-hadar sa ta kudi ba.

Shugaban babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya ce sun samu labari kawai daga kafar labaru na sauya hukumar bankin ta Frist.

CBN ya ce bankin na da tasgaro ga lamuran bashi da sauran harkokin cikin gida.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *