• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRAMINISTAN SUDAN ABDALLAH HAMDOK YA YI MURABUS YAYIN DA ZANGA-ZANGA KE RURUWA

ByNoblen

Jan 3, 2022 ,

Firaministan Sudan Abdallah Hamdoz ya yi murabus daga mukamin sa yayin da masu zanga-zangar kin jinin mulkin soja ke kara dagewa.
Hamdok ya sanar da murabus ne bayan wata biyu da kwace madafun iko da sojoji karkashin Janar Abdel Fatah Al-Burhan su ka yi.
In za a tuna an tsare Hamdok lokacin juyin mulkin a ranar 25 ga watan Oktobar bara, inda daga bisani a ka samu yarkjejeniya har Hamdok ya sake dawowa mukamin sa.
Yanzu dai sojojin ke rike da madafun ikon Sudan gam inda su ke dirar mikiya kan masu zanga-zanga.
Hamdok ya ce ya yi iya bakin kokarin don dawo da kasar kan tsarin da zai kai ga gudanar da zabe don samun gwamnatin farar hula a 2023.
Sudan ta shiga rudanin siyasa da mulki tun kawar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Janar Omar Hassan Elbashir a 2019.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *