Firaministan Lebanon Najib Mikati na yunkurin shawo kan kasashen Larabawa su amince da dawo da dangantaka yanda ya dace da kasar mai fama da kalubalen tattalin arziki.
Matakin na Mikati ya biyo bayan ziyarar da shugaban Faransa Emmanuel Macron zuwa Saudiyya don shiga tsakani warware yanke huldar jakadanci da Saudiyya ta yi da Lebanon.
In za a tuna Saudiyya ta janye jakadan ta daga Lebanon da korar jakadan Lebanon don kalaman da ministan labarun Lebanon George Kordahi ya yin a caccakar Saudiyya kan yaki da ‘yan tawayen houthi ‘yan shi’a a Yaman.
Bayan tsanantar yanayin, Kordahi ya yi murabus daga mukamin sa inda Mikati ya cigaba da ba wa Saudiyya da sauran kasashen larabawa da su ka marawa Saudiyya baya hakuri.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀