• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRAMINISTAN LEBANON MAI JIRAN GADO ZAI SHIGA TATTAUNAWA DON KAFA GWAMNATI MAI KWARI

Sabon firaministan Lebanon mai jiran gado Mustapha Adib na daukar matakan gudanar da tattaunawa don kafa gwamnatin mai kwari da za ta farfado da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare.Adib na son biyewa tsarin Faransa ne da ke taimakon kasar ta hanyar  tsame hannun ministocin da zai nada daga iyayen gidan su na gidajen siyasar kasar. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci birnin Beirut bayan fashewar makamai a tashar jirgin ruwa da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 300. A tsarin Lebanon firaminista kan zama musulmi dan Ahlusunnah, shugaban majalisar dan Shi’a inda shugaban kasa kan fito daga mabiya addinin kirista. Shugaban Lebanon Michel Aoun ya hori Adib da kafa gwamnati don ceto kasar daga matsalolin tattalin arziki. Adib dai dan wata karamar jam’iyyar siyasa ne ta ‘yan sunna da tsohon firaministan kasar Najib Mikati ke jagoranta. Mustapha Adib wanda shi ne jakadaan Lebanon a Jamus tun 2013, ya samu mara bayan babbar jam’iyyar Ahlusunnah ta marigayi Rafik Hariri da Saudiyya ke marawa baya. Hakanan ya samu goyon bayan ‘yan majalisa mabiya Shia da Hezbollah mai samun goyon bayan Iran ke da tasiri a kan su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “FIRAMINISTAN LEBANON MAI JIRAN GADO ZAI SHIGA TATTAUNAWA DON KAFA GWAMNATI MAI KWARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.