• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRAMINISTAN LEBANON MAI JIRAN GADO YA BAR GADON BAYAN WATA DAYA

ByNoblen

Sep 27, 2020

Sabon firaministan Lebanon Mustapha Adib ya yi murabus bayan wata daya da fara aikin kafa gwamnatin da ya ce ta kwararru ce.
Adib a jawabi da a ka yayata ta gidan talabijin, ya ajiye mukamin ne cikin rudani bayan ganawa da shugaban kasar Michel Aoun.

Murabus din Adib ya tsunduma Lebanon cikin yanayi na rashin tabbas.
Da alamun Adib ya kasa samun nasara saboda yanda jam’iyyar ‘yan shia ta Hezbollah da Iran ke marawa baya da takwarar ta ta Amal su ka dage sai sun samu jan ragamar mukamin ma’aikatar kudi.

Lebanon da kan yi shugaba mabiyin addinin kirista, firaminista musulmi Ahlusunnah da majalisa bisa jagorancin shia, ta shiga sabon yanayin zullumin hada kan kasar bayan tashin boma-bomai a tashar teku da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 200.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “FIRAMINISTAN LEBANON MAI JIRAN GADO YA BAR GADON BAYAN WATA DAYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.