• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRAMINISTAN ISRAILA BENNETT YA SAUKA A DAULAR LARABAWA

ByNoblen

Dec 13, 2021

A karon farko firamistan Israila Naftali Bennett ya sauka a Abu Dhabi, Daular Larabawa don ziyara ta musamman tsakanin kasar yahudawa da ta larabawa.
Ministan harkokin wajen Daular Abdullah bin Zayed Al-Nahyan ne ya tarbi Bennett a filin jirgi.
Ziyarar ta zo ne biyo bayan yarjejeniyar nan ta 2020 da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranta, inda wasu kasashen larabawa su ka kulla diflomasiyya da Israila a yarjeniyar da a ka lakabawa suna “yarjejeniyar Ibrahim.”
A watan Maris, Daular Larabawa ta sanar da kulla huldar zuba hannun jarin ta a Israila na dala biliyan 10.
Palasdinawa na kin jinin wannan yarjejeniya ta “Ibrahim” da ke nuna ‘yan uwan su larabawa sun kulla kawayen su da yahudawa masu gana mu su azaba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *