• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRAMINISTAN IRAKI YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA A HARIN JIRGI MARAR MATUKI

ByNoblen

Nov 8, 2021

Firaministan Iraki Mustapha Alkhadimi ya tsallake rijiya da baya a harin jirgi marar matuki da a ka kai kan gidan sa.

Alkadhimi dai ya tsira ba tare da samun rauni ba a harin da a ka tabbatar don neman hallaka shi ne.

Tuni firaministan ya bukaci a kwatar da hankali da kuma neman tattaunawa don sulhunta rashin zaman lafiyar kasar.

Saudiyya da sauran kasashen larabawa sun yi tir da harin.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yabawa jajircewar firaministan kan harin na ta’addanci, ya na mai nuna ajiyar zuciya hakan bai shafi lafiyar firaministan ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.