• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FIRAMINISTAN BURTANIYA BORIS JOHNSON YA SAUKA A RIYADH

Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya sauka a babban birnin Saudiyya, Riyadh inda Yarima Muhammad bin Salman ya yi ma sa maraba.
Burtaniya da Saudiyya za su sanya hannu kan muhimman yarjejeniyar huldar da za ta kawo riba tsakanin kasashen biyu.
Johnson na ziyarar yankin gabar ta tsakiya don tabbatar da samun fetur ba tare da tangarda ba, da kuma matsa lamba kan shugaban rasha Vladimir Putin don ya janye daga mamaye Ukraine.
Hakika mamaye Ukraine da Rasha ta yi ya jawo tashin farashin gangar man fetur a duniya da ya sanya kasashe daidaita hanyoyin samun man.
Johnson na bukatar karfafa kasuwancin makamashi waje da man fetur, inda a gefe guda ya ke bukatar Saudiyya ta cike gurbin bukatun man na Burtaniyya don ta rage dogaro kan Rasha.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “FIRAMINISTAN BURTANIYA BORIS JOHNSON YA SAUKA A RIYADH”
  1. If you desire to increase your familiarity simply keep visiting this
    web site and be updated with the newest gossip posted here.

Leave a Reply

Your email address will not be published.