• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FILATO TA SOKE SUFURI DA BABURA WARO ACHABA

Byadmin

Jul 27, 2021 , , ,

Gwamnatin jihar Filato ta soke sufurin babura wato achaba inda kuma ta takaita sufurin keke-napep zuwa karfe 7 na yamma.

Lamarin ya shafi cikin garin Jos da Bukur.

Sakataren gwamnatin jihar Danladi Atu ya ce matakin don inganta lamuran tsaro don hana amfani da hanyar sufurin wajen aikata miyagun laifuka.

Atu ya ce za a yi wa ‘yan keke-napep da masu baburan rejista da yin fenti don bambance kananan hukumomin masu aiki da su. 

Gwamnatin jihar za ta yi zama da kungiyoyin masu sufurin don baiyana muradun daukar matakin.

An zargi ma’abota wannan sufuri da taimakawa wajen fauce wayoyin salula da jakar mata har ma da sanadiyyar rasa rayuka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,439 thoughts on “FILATO TA SOKE SUFURI DA BABURA WARO ACHABA”