• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FICEWA DAGA KOTU DA LAUYOYIN KANU SU KA YI YA JAWO TSAWAITA SHARI’A

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 11, 2021

Ficewa daga kotu da lauyoyin shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu su ka yi gabanin isowar alkali Jostis Binta Nyako ya jawo daga lokacin sauraron karar.
Yanzu dai kotu ta sanya ranar 19 ga watan Janairun badi a matsayin ranar dawowa kotu.
Lauyoyin karkashin Ifeanyi Ojiofor sun fice daga kotun ne don fusata da yanda jami’an tsaron DSS su ka hana daya daga lauyoyin da su ke tare dan Amurka Bruce Fein shiga kotun.
Duk da haka lauyoyin sun nuna bacin rai ga yanda kotun ta zauna duk da boren da su ka nuna na ficewa.
Da alamu lauyoyin Kanu sun haddasa wahalar da shari’ar da a ke tuhumar Kanu da ta shafi cin amanar kasa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.