• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FAYEMI YA GANA DA SHUGABA BUHARI A FADAR ASO ROCK KAN LAMURAN TSARO

Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buharu a fadar Aso Rock kan lamuran tsaro.

Fayemi wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnoni, ya tattauna da shugaban kan buatar odar makamai inda ya ce nan gaba kadan shugaban zai tura kuduri gaban majalisa don sayo makamai.

Duk da wannan bai shafi rashin ganin makamai a kasa ba, kamar yanda mai ba da shawara kan tsaro Babagana Monguno ya fada, amma ya nuna akwai damuwa cewa miyagun iri kan mallaki makamai masu illar gaske da tunkarar su sau an shirya sosai.

Fayemi ya nemi ture tunanin jama’a cewa shugaba Buhari bai san ainihin abun da ke faruwa a kasar ba, ya ce a zantawar sa da shugaban ya fahimci shugaban ya san duk abun da ke faruwa a Najeriya har ma da wasu bayanai da ba a sani ba.

Fayemi ya kara da cewa shugaban ya amince da samawa dakarun tsaro kayan aiki don taimakawa sabbin manyan hafsoshi su cimma nasarar samar da tsaro mai inganci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “FAYEMI YA GANA DA SHUGABA BUHARI A FADAR ASO ROCK KAN LAMURAN TSARO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.