• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FASA RUMBUNAN ABINCI YA ISO ABUJA INDA A KA YI AWUN GABA DA BUHUNAN ABINCI, TALIYA DA TAKIN ZAMANI

Yanayin fasa rumbunan gwamnati na abinci ya iso yankin Abuja bayan hakan ya fara zama ruwan dare a wasu jihohi da masu dibar Kayan ke daukar hakan a matsayin ganima.

Lamarin yanzu ya wuce tunkarar kayan abinci, don a Abuja har takin zamani a ka wawashe.

Zuwa yanzu an tabbatar da asarar rayuka a babbar wawar da a ka yi a Abuja a garin Gwagwalada inda mutane su ka yi dafifi da fasa rumbun abinci da ya jawo turereniyar da ta haddasa rasa rayuka da samun raunuka.

Alhaji Halliru Auta, basaraken Doshin Paikon Kore ne a yankin Gwagwalada da ya bugi jaki da takin ta hanyar nuna ko ma za a debi kaya kar su wuce na abinci.

Halliru Auta wanda limamin masallacin Gwarawa ne da a idon sa a ka wawashe kayan, ya bukaci gwamnati ta rika kula da walwalar al’umma.
Gwamnatin birnin Abuja ta zaiyana wadanda su ka fasa rumbunan da cewa masu aikata laifi ne don ita tuni ta kammala raba kayan tallafin korona bairos.

Alhaji Abbas G. Idris shi ne shugaban hukumar agajin gaggawa na Abuja da ke cewa sun rubuta rahoton duk tallafin da a ka bayar.

A yanzu dai akwai alamun gwamnati da sauran cibiyoyin adana abinci a Abuja na sauyawa kayan abinci wajen zama don gudun masu warwaso.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “FASA RUMBUNAN ABINCI YA ISO ABUJA INDA A KA YI AWUN GABA DA BUHUNAN ABINCI, TALIYA DA TAKIN ZAMANI”
  1. When I originally commented I clicked the “Notify me when new comments are added” checkbox and now each
    time a comment is added I get four e-mails with the same comment.
    Is there any way you can remove people from that service?
    Bless you!

Leave a Reply

Your email address will not be published.