• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FASA JANYE TALLAFI-HAR YANZU GIDAJEN MAI BA SU MIKE DAIDAI BA A ABUJA

Kusan mako daya bayan fasa janye tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi, gidajen mai a Abuja ba su dawo daidai ba.
Yayin da wasu gidajen man ke rufe wasu kuma na sayarwa amma da layuka na masu son shan man don firgicin kar ya yanke.
A gefen gidan man TOTAL na AREA 11 a kan ga matasa da jarakunan man su na sayar da man da tsada ga wadanda ba su da hakurin jiran dogon layi.
Hakanan wasu kan dau jarakuna su sa a mota don bayan sun cika tankin mota su cika jarakunan kuma ba lalle ba ne don amfanin janareta ba ne.
Ba mamaki mutane ma sun taimaka wajen samun cikas a gidajen man don yanda su kan bazama su taru a duk gidan man da ke da mai a lokaci daya alhali ba lalle ba ne an rasa man gaba daya ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “FASA JANYE TALLAFI-HAR YANZU GIDAJEN MAI BA SU MIKE DAIDAI BA A ABUJA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.