• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FARAWA DA IYAWA AMNESTY TA CACCAKI SABON SHUGABAN IRAN RAISI

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty ta soki sabon shugaban Iran Ebrahim Raisi da kisan gilla, gallazawa da batar da mutane.

Amnesty ta fitar da matsaya ne kan Raisi jim kadan bayan aiyana a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da wasu su ka ki jefa kuri’a ciki har da tsohon shugaban kasar Ahmadinejad.

Kumgiyar Amnesty ta yi mamakin, maimakon a ce an cafke Raisi ya fuskanci tuhuma sai a ka ba shi dama ya zama shugaban Iran.

Kungiyar ta ce ta wallafa wani rahoton hannun Raisi dumu-dumu a wata tawagar da ta kashe dubban ‘yan hamaiya a gidajen yarin Evin da Gohardasht a 1988.

Kazalika a matsayin sa na jagoran shari’a, Raisi ya yanke hukuncin garkamewa na gayawa jini na wuce kan dururuwan masu zanga-zanga, ‘yan kare hakkin dan adam da marar sa rinajye.

An tabbatar an murde zaben ta yanda Raisi zai zama sabon shugaba don an ki wanke wasu ‘yan takara.

Ebrahim Raisi zai karbi ragamar Iran daga hannun shugaba mai barin gado da a ke ganin ya na da matsakaicin tsaurin ra’ayin muradun shia Hassan Rauhani a watan agusta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “FARAWA DA IYAWA AMNESTY TA CACCAKI SABON SHUGABAN IRAN RAISI”
  1. Thanx for the effort, keep up the good work Great work, I am going to start a small Blog Engine course work using your site I hope you enjoy blogging with the popular BlogEngine.net.Thethoughts you express are really awesome. Hope you will right some more posts.

  2. If some one wants expert view regarding blogging and site-building then i suggest him/her to
    go to see this weblog, Keep up the nice job.

Leave a Reply

Your email address will not be published.