• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FARAFAGANDAR KAYRA TA HADDASA YAKIN IRAKI-INJI GWAMNATIN NAJERIYA

A cigaba da caccakar gidan talabijin na CNN don labarin da ya yada na nuna sojoji sun yi kisan gilla ga masu zanga-zangar ENDSARS a Lekki, gwamnatin Najeriya ta ce yada labarun karya su ka jawo yakin Iraki.

Ministan labarun Najeriya Lai Mohmmed ya zargi CNN da yada labarun karya kan Iraki da cewa ta mallaki makamai na kisan kare dangi, da hakan ya jawo Amurka jagorantar aukawa kasar da yaki.

Mohammed ya ce ya zama wajibi a hana labarun da ba su da sahihanci don gudun haddasa fitina ta hanyar da za a iya kaucewa.

Ministan ya nuna damuwar gwamnatin Buhari ga CNN da cewa ta saba muhimmiyar ka’idar kafar sadarwa ta sauraron dukkan sassa kafin yada labari.

In za a tuna gidan talabijin na CNN ya ce ya na kan bakar sa cewa labarin da ya yada gaskiya ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “FARAFAGANDAR KAYRA TA HADDASA YAKIN IRAKI-INJI GWAMNATIN NAJERIYA”
  1. When I originally commented I clicked the “Notify me when new comments are added” checkbox and now each time a comment
    is added I get several emails with the same comment.
    Is there any way you can remove me from that service?
    Cheers!

Leave a Reply

Your email address will not be published.