• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FADAR GWAMNATIN NAJERIYA TA CACCAKI OTOM DA YADA KIYAIYAR KABILANCI

Fadar gwamnatin Najeriya ta caccaki gwamnan jihar Binuwai Samuel Otom da zargin sa da yin kalamai na yada kiyaiya.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya ce Otom na kalaman tada fitina tamkar yanda ya faru a Rwanda inda a ka samu kisan kare dangi na kabilanci.

Shehu ya ce kamar yanda ‘yan kabilar Hutu a Rwanda su ka yada cewa akwai wata makarkashiya da kabilar Tutsi ke kullawa har hakan ya kawo kisan kare dangi; hakanan shi ma Otom ke yi inda a jihar sa da kasa gaba daya ke cewa akwai ajanda ta maida Najeriya karkashin mulkin Fulani.

Sanarwar ta ce Otom na kalaman ne don kare shirin sa na son zuciya na kafa gonakin kiwon shanu.

Fadar gwamnati ta ce gwamnan da kan canza jam’iyya don rashin akida, ya jawo al’ummar sun yi rashin sa’a don yanda Otom din ya yada kiyaiyar kabilanci da ta bangaranci.

Irin wannan, a ra’ayin fadar ya nuna Otom bai dace da rike mukamin jagorantar al’umma ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “FADAR GWAMNATIN NAJERIYA TA CACCAKI OTOM DA YADA KIYAIYAR KABILANCI”
 1. Thanks for finally writing about > FADAR GWAMNATIN NAJERIYA TA CACCAKI OTOM DA YADA KIYAIYAR KABILANCI – Noblen tv < Liked it!

 2. Hey There. I found your weblog using msn. That is a really well
  written article. I’ll be sure to bookmark it and come back to read more of your
  helpful information. Thanks for the post. I will definitely return.

 3. Hello there! This is my first comment here so I just wanted to give a
  quick shout out and tell you I truly enjoy reading your
  posts. Can you suggest any other blogs/websites/forums that go over
  the same subjects? Thank you!

Leave a Reply

Your email address will not be published.