• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FADAR GWAMNATI TA CE WASU ‘YAN NAJERIYA SUN TARU A LONDON DON MARAWA SHUGABA BUHARI

ByYusuf Yau

Apr 6, 2021

Fadar gwamnatin Najeriya ta baiyana cewa wasu ‘yan Najeriya sun taru a gidan Najeriya da ke London wato ofishin jakadancin Najeriya don mars baya ga shugaba Buhari.

Wannan ya biyo bayan yanda wasu karkashin mai taimakawa tsohon shugaban Najeriya Reno Omokri su ka gudanar da zanga-zangar adawa da shugaban.

A yanzu haka shugaba Buhari na London don ganin likita.

Masu zanga-zangar adawa da shugaban na nuna bai dace ya taho har London neman magani ba, da ya dace ya zauna a gida ya ga likita.

Masu mara baya na nuna shugaban ya yi aiyuka da dama ga irin jibgin matsalolin da ya samu lokacin da ya hau karagar mulki.

Sabuwar zanga-zangar tamkar martani ne ga su Omokri da su ke caccakar shugaban kan lamuran da ba za su rasa nasaba da siyasa ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *