• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

FACEBOOK ZAI RABAWA KANANAN ‘YAN KASUWA TALLAFI A NAJERIYA

A ranar Litinin da ta gabata ne kamfanin manhajar dandalin sada zumunta na ‘Facebook’ ya sanar da shirin fara rabawa kananan ‘yan kasuwa 781 a Najeriya tallafin miliyan N500.

Shirin bayar da tallafin na daga cikin tsarin kamfanin ‘Facebook’ na rabawa kananan ‘yan kasuwa 30,000 a kasashen duniya fiye da 30 tallafin dalar Amurka $100m, kamar yadda ya sanar a farkon shekarar 2020.

Har yanzu manhajar ‘Facebook’ ce a gaba idan ana maganar kamfanonin da suka mallaki manhajojin da ake yi wa ‘kudin goro’ ta hanyar kiransu da sunan dandalin sada zumunta.

Kamfanin ‘Facebook’ ya sanar da cewa zai bayar da tallafin ne domin taimakawa jama’a wajen farfadowa daga kangin matsin tattalin arziki da aka shiga sakamakon bullar annobar korona.

A cewar kamfanin, an zabi bayar da tallafin ga kananan ‘yan kasuwa ne saboda sun fi jin jiki sakamakon tasirin annobar korona.

Kamfanin Deloitte tare da hadin gwuiwar FATE Foundation da Afrigant ne zasu kula tare da raba tallafin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Za a bayar da tallafin kudi da damar tallata hajar ‘yan kasuwa kyauta domin taimakawa kananan ‘yan kasuwa a yayin da suke shirin farfadowa bayan kalubalen da wannan shekarar ta zo da shi,” a cewar sanarwar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube kaitsaye a shafinmu.
Na face book, ko Instergram na Noblentv
Ko
Kai tsaye a a www.noblentv.co.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “FACEBOOK ZAI RABAWA KANANAN ‘YAN KASUWA TALLAFI A NAJERIYA”
  1. Hi! Someone in my Myspace group shared this site with
    us so I came to look it over. I’m definitely loving the information. I’m book-marking and will be
    tweeting this to my followers! Terrific blog and superb design and style.

Leave a Reply

Your email address will not be published.