• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: ZA MU RAMA DUK WATA CUTARAWA DA ‘YAN KUDU SU KA YI MANA

Shugaban wata kungiyar kare muradun arewa maso gabashin Najeriya Abdulrahman Kwacam ya yi barazanar jama’ar sa za su rama duk wata cutarawa da wasu daga kudu su ka yi wa ‘yan arewa a nan gaba.

Kwacam wanda ke magana a taron wata-wata na zauran muryar Amurka a Abuja akan darussan zanga-zangar endsars, ya baiyana takaicin yanda wasu tsagera su ka kona dukiyoyin ‘yan kasuwar arewa a kudancin Najeriya lokacin zanga-zangar da ya ke ganin tsananin rashin adalci ne.

Abdulrahman Kwacam wanda bai baiyana dalla-dalla hanyar da za su yi ramuwar ba, ya bukaci jami’an tsaro su zama shaida kan batun da ya ce a gyara kafin lamarin ya sake aukuwa.

Nan take dan kabilar Igbo a wajen taron Igwe Martin ya ce akwai gyara a tunanin na Kwacam, don lamarin barazana ga rayuka ko kona dukiya na faruwa ne daga miyagun iri da ba ruwan su da bambancin kabila ko yanki.

Martins ya bukaci gwamnati ta yi tsayin daka wajen hukunta duk wanda a ka samu da laifi ba tare da la’akari da ko waye ke daure ma sa baya ba.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ACP Aminu Garba da ya wakilici kwamishinan ‘yan sanda na Abuja a taron, ya ce ba daidai ne duk wani mataki na daukar doka a hannu ba tun da hukuma ce ke da hakkin kare jama’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
6 thoughts on “ENDSARS: ZA MU RAMA DUK WATA CUTARAWA DA ‘YAN KUDU SU KA YI MANA”
 1. Excellent article. Keep writing such kind of information on your page.
  Im really impressed by your blog.
  Hey there, You have done a great job. I’ll definitely digg it and personally suggest
  to my friends. I’m confident they’ll be benefited from this web
  site.

 2. Howdy! This is my first comment here so I just wanted to give a quick shout out and
  say I genuinely enjoy reading your articles. Can you recommend any other blogs/websites/forums that deal with the same topics?
  Thanks a lot!

 3. Great beat ! I would like to apprentice even as you amend your site, how
  can i subscribe for a blog site? The account aided me a
  applicable deal. I have been tiny bit acquainted of
  this your broadcast offered bright transparent idea

 4. Hello! I just wanted to ask if you ever have any problems with hackers?
  My last blog (wordpress) was hacked and I ended up losing months of hard work due to no back up.

  Do you have any methods to prevent hackers?

Leave a Reply

Your email address will not be published.