• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: ‘YAN SANDA SUN TARWATSA ZANGA-ZANGA A GOMBE

Jami’an ‘yan sanda sun kawar da ‘yan zanga-zangar #endsars# a Gombe bayan da matasan su ka fito da hawa kan titi.
‘Yan zanga-zangar da run farko sun sanar da za su shiga zanga-zangar da ke neman zama ta kasa gaba daya, sun taru a muhimmiyar mashigar Gombe daga Bauchi da a ka fi sani da MIL 3 ko sabon suna “rainbow round-about” inda su ka fara jawo tsaikon motoci.
Da alamun masu zanga-zangar sun yi juyawa da bayan rago ne don sake sako.

A daidai lokacin rubuta wannan labari an girke motocin ‘yan sanda a mashigar don hana cigaba da zanga-zangar.
Za a iya cewa yunkurin yin zanga-zangar a Gombe ka iya shafar wasu sassan jihohi 6 na arewa maso gabar don zaman jihar a tsakiyar sauran jihohin da kuma zama cibiyar kasuwanci.

Hakanan jihar ta zama tudun mun tsira ga ‘yan gudun hijira daga jihar Borno lokacin da fitinar Boko Haram ta ta’azzara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.