• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: ‘YAN NAJERIYA NA JIRAN SAKAMAKON BINCIKE

Daidai lokacin da jihohi ke tattara bayanai na korafin jama’a kan yanda ‘yan sandan SARS da a ka rushe su ka ci zarafin su, bukatar ta kara fadi ta neman yin garambawul ga dukkan sassan ‘yan sanda don hana al’adar amfani da kayan sarki wajen cin zali ko danne hakkin ‘yan-adam.

Duk da a na  cewa ‘yan sandan sun yi karanci in an duba yawan ‘yan Najeriya, amma a kan gan su barkatai tare da manyan jami’an gwamnati su na tafiya da ke barazana ga sauran masu amfani da tituna.

Abubakar Shumo wanda ya shiga hannun ‘yan SARS a Abuja, ya baiyana yanda hatta gawa a likkafani ba ta tsira daga wuce gona da iri na SARS ba.

Marigayi mai kama barayi Alhaji Ali Kwara ya baiyana zamba cikin aminci da wani dan SARS ya yi da hakan ke kara tabbatar da cin hanci da rashawa a rusasshiyar rundunar.

Ga ‘yan sandan da ba ma na SARS ba, a Bauchi a na jiran sakamakon binciken DPO Baba Ali Muhammed da a ka zarga da dukan kawo wuka ga yara 3 har biyu su ka mutu sabadiyyar satar kaza.

Kakakin rundunar a Bauchi DSP Muhammad Wakili ya ce an kafa kwamitin bincike.

Ministan ‘yan sanda Maigari Dingyadi ya ce sam ba za a amince sabuwar rundunar da ta maye SARS wato SWAT ta mallaki jami’an marar sa imani ba.

Da alamu jami’an ‘yan sanda masu zafin kai kan tabuka abun kirki a jihohin da ke da kalubalen ‘yan ta’adda ne don yaki da ta’addancin, amma su kan huce kan farar hula a jihohin da ba su barazanar ‘yan ta’addan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “ENDSARS: ‘YAN NAJERIYA NA JIRAN SAKAMAKON BINCIKE”
 1. Pretty great post. I just stumbled upon your blog and wanted to say that I have truly enjoyed surfing around your blog posts.
  After all I’ll be subscribing to your rss feed and I hope you write again very
  soon!

 2. Howdy! This is my first comment here so I just wanted to give a quick shout out and
  say I really enjoy reading through your blog posts.
  Can you suggest any other blogs/websites/forums that
  cover the same subjects? Appreciate it!

 3. I am extremely impressed with your writing skills and also with the layout on your blog.
  Is this a paid theme or did you customize it yourself?
  Either way keep up the nice quality writing, it is rare to see a
  nice blog like this one today.

Leave a Reply

Your email address will not be published.