• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: MU DAI LABARIN MU NA HARBE-HARBE A LEKKI GASKIYA NE – INJI CNN

Gidan talabijin na CNN ya ce ya na kan bakar sa kan labarin da ya yada na shaidar kashe-kashe a Lekki lokacin zanga-zangar ENDSARS.

Gidan talabijin din ya yada hirarraki, faya-fatan bidiyo da hotuna da ke nuna bude wuta kan masu zanga-zangar.

CNN na maida martani ne kan matsaar ministan labarun Najeria Lai Muhammed da ke watsi da labarin da kuma bukatar a gwale CNN.

Ministan ya ce face kwamitin binciken lamarin ya kammala aiki, ba za a iya dorar da wani batu ba da ya wuce duniya ta shaida labarin sojoji sun yi kisan kiyashi amma ba gawawwakin wadanda a ka ce an kashe.

In za a tuna sojoji sun ba da shaidar cewa sun yi harbi a Lekki amma da albarusan roba da ba sa kisa sai dai illa ta kona fata ko in an harba kan idon mutum.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “ENDSARS: MU DAI LABARIN MU NA HARBE-HARBE A LEKKI GASKIYA NE – INJI CNN”
 1. An outstanding share! I’ve just forwarded this onto a coworker who had
  been doing a little homework on this. And he in fact bought me breakfast
  simply because I discovered it for him… lol.
  So allow me to reword this…. Thank YOU for the meal!!
  But yeah, thanks for spending time to talk about this matter here on your internet site.

 2. Hi, Neat post. There’s an issue with your website in web explorer, would check this?
  IE nonetheless is the market chief and a large
  section of folks will miss your excellent writing due to this problem.

Leave a Reply

Your email address will not be published.