Lamarin zanga-zangar kawo karshen SARS a jihar Edo ya zama da akasin gaske inda a ka fasa gidan yari fursunoni su ka fice.
Masu zanga-zangar kan tare muhimman hanyoyi da dafa abinci a gefen titi.
Sabon salon da ya kai ga fasa gidan yari ya sanya gamaiyar kungiyoyin matasan arewa janye zanga-zangar kawo karshen rashin tsaro a jihohin arewa 19.
An samu karin muradun zanga-zangar fiye da batun kawo karshen zaluncin jami’an ‘yan sanda inda lamarin ta hada da neman garambawul ga kasa.
Dattawa da masu sharhi na nuna fargabar zanga-zangar ka iya jefa Najeriya a cikin rudanin da sai an yi da gaske kafin kawo maslaha.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I needed to thank you for this excellent read!! I definitely
enjoyed every bit of it. I have you bookmarked to look at new stuff you post…