• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: BA ZA MU BARI A SAKE SAMUN ZANGA-ZANGAR BA – DINGYADI

Ministan ‘yan sandan Najeriya Maigari Dingyadi ya ce gwamnati ba za ta bar lamarin zanga-zangar kawo karshen SARS ya sake aukuwa ba.

Ministan na magana ne bayan taron tsaro a fadar Aso Rock da shugaba Buharu ya jagoranta.

Ministan ya kara da cewa gwamnati za ta cigaba da sauraron al’umma ta hanyar tattaunawa da ganawa da matasa, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ‘yan siyasa da ma ma’aikata.

Taron ya cimma matsayar inganta aikin ‘yan sanda da ba su kayan aiki don samun kuzarin tsaron rayuka da dukiyar jama’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.