• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: BA SUNAN AISHA YESUFU A JERIN SUNAYEN DA BABAN BANKIN NAJERIYA CBN YA SAMU HURUMIN RUFE AJIYAR SU TA BANKI

Babbar kotun taraiyar Najeriya ta Abuja ta amince da bukatar babban bankin Najeriya CBN na rufe ma’ajiyar bankin mutum 19 da wani kamfani daya da ke tallafawa zanga-zangar endsars amma ba a ga sunan Aisha Yesufu da a ka yi ta yayatawa a yanar gizo na mara baya ga zanga-zangar ba.

Da alamu dai duk sunayen mutanen 19 ‘yan yankin kudancin Najeriya ne.

Babbar kotun ta ba da dama a rufe ma’ajiyar  mutanen 19 har sai  watan Janairu na badi kuma ba mamaki a iya tsawon wa’adin bayan kammaluwar lokacin horon.

Ba cikkeken bayanin ko nawa ne wadanda a ka dakatar da aikin ma’ajiyun na su ke da shi a banki kuma ko na wa a ka fitar da ma’ajiyun don tallafawa zanga-zangar da ta juye kona dukiya da ma kisan gilla.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.