• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS-AN KAWO BAYANAN GAWAWWAKI 99 DA A KA KAI ASIBITI A LAGOS A OKTOBA 2020

ByNoblen

Jul 11, 2021 , , ,

Babban jami’in binciken kwayoyin halitta na gwamnatin jihar Lagos Farfesa John Obafunwa ya baiyana gaban kwamitin binciken zaluncin ‘yan sanda na ENDSARS a Lagos  da sakamakon binciken gawawwaki 99 da a ka tattara a sassan Lagos tsakanin 20-27 ga watan Okotobar bara.

Sakamakon ya nuna uku ne kadai daga dukkan gawawwakin a ka rubuta cewa an zi da su daga Lekki da a ke zargin sun mutu ne sakamakon bude wuta da jami’an tsaro su ka yi kan masu zanga-zanga.

Zuwa yanzu gawawwakin uku maza ba a gano ko su waye ba ne.

Kungiyoyi da masu zanga-zangar sun yi zargin an yi kisan kiyashi a Lekki lokacin zanga-zangar Endsars.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *