Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya kafa kwamitin binciken irin illar da ‘yan sanda su ka samu a sanadiyyar zanga-zangar endsars.
Kwamitin mai mutum 9 zai binciko asarar rayuka da dukiyar rundunar a fadin taraiyar Najeriya.Kwamitin na karkashin jagorancin CP Abutu Yaro, zai ziyarci duk wajajen da a ka samu akasi da kuma zuwa gidajen jami’an da lamarin ya rutsa da su don jajantawa iyakin su.
Sakamakon rahoton kwamitin zai taimaka ne wajen tsare-tsare na nan gaba da kuma sake damarar ‘yan sanda.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀