• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ENDSARS: AN AIYANA DOKAR HANA YAWO

Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya aiyana dokar hana yawo dare da rana a jihar bayan zanga-zangar kawo karshen SARS ta juye zuwa kone-kone.
Gwamnatin ta kafa dokar a daidai lokacin da zanga-zangar ke fantsama wasu sassan kasar.
Masu zanga-zangar sun cinnawa wani ofishin ‘yan sanda a Lagos wuta da kuma barazana ga kadarorin gwamnati.

Labari ya nuna dan sanda daga ofishin na Orile ya harbe wani mai zanga-zanga da hakan ya fusata masu zanga-zangar su ka cinnawa ofishin wuta da hakan ya sanya jami’an shigar burtu su ka arce daga ofishin.
Yanzu haka ma an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja.

Wannan na nuna kutsowar masu tada fitina a cikin zanga-zangar da ta fara cikin ruwan sanyi da hatta a jihar Osun gwamna Gboyega Oyeyola ya halarci dandalin zanga-zangar amma ya sha da kyar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “ENDSARS: AN AIYANA DOKAR HANA YAWO”
  1. What’s Going down i’m new to this, I stumbled upon this I’ve found It positively helpful and it has aided me out loads.

    I’m hoping to contribute & assist different customers like its aided me.
    Great job.

  2. Hi there all, here every person is sharing these knowledge, therefore it’s pleasant to read
    this webpage, and I used to pay a visit this webpage every day.

Leave a Reply

Your email address will not be published.