• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

EMEFILE YA BAIYANA MURADUN SA NA NEMAN ZAMA SHUGABAN NAJERIYA

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya baiyana muradun sa na zama shugaban Najeriya bayan amincewa da zai gwada takarar a inuwar APC.

Tuni wasu manoma da ke ganin ya taimaka da lamunin da ya sa su ka samu riba su ka yi tayin saya ma sa fom kan Naira miliayn 100.

Emefiele a sako ta shafin sa na tiwita, ya godewa manoman inda ya ce ya amsa kiran su amma zai yi amfani da kudin da ya tara na kashin kan sa a tsawon aikin banki na shekaru 35 don sayan fom din.

Wannan na faruwa daidai lokacin da wasu da ke ganin bai dace gwamnan banki ya yi takara ba, ke kira ga shugaba Buhari ya kwabe shi daga mukamin.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP na bukatar a cafke Emefiele da hukunta shi bisa abubuwan da ya aikata a baya a jagorancin babban bankin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.