Shugaban Masar Abdelfatah Alsisi da shugaban Yaman Rashad Al-Alimi sun gana kan batun tsaron tekun bahar maliya da ke fuskantar hare-hare.
Shugabannin biyu sun gana a birnin Alkahira na Masar inda su ka karfafa batun tsaron bahar maliya biyo bayan hare-hare da barazana da Iran ke yi wa jiragen dakon mai.
Elsisi ya karfafa gamaiyar tsaro a bahar maliya da mashigar babal mandab don jiragen ruwa su samu ‘yancin sufurin su ba tare da cikas ba.
Elsisi ya jaddada goyon baya ga halaltacciyar gwamnatin Yaman da ke birnin Aden, ya na mai zaiyana Yaman da kofar Larabawa da wayewa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀