• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ELON MUSK YA SAYI KAMFANIN TWITTER DALA BILYAN 44

Dan kasuwar nan Elon Musk ya sayi kamfanin sadarwar nan na yanar gizo TIWITA kan zunzurutun kudi dala biliyan 44.
Kamfanin na tiwita ya tabbatar da wannan ciniki inda ya ce a yanzu zai zama mai zaman kan sa don yanda dan kasuwar ya saye shi.
Elon Musk wanda shi ya fi kowa kudi a duniya, ya ce ya zabi sayen tiwita don ya na ganin har yanzu kamfanin bai kai ganiyar cimma burin kafa shi ba.
Musk ya ce lalle tiwita ta zama babban dandalin damar fadar albarkacin baki da gina amintaka tsakanin kamfanin da masu hulda da shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.