• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

El-Rufai ya sauya tsarin aikin gwamnatin Kaduna, za a koma aikin kwana 4 a mako

ByAuwal Ahmad Shaago

Nov 29, 2021

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sabon tsarin aikin gwamnati a jihar inda za a dinga aikin kwanaki hudu a mako Kamar yadda El-Rufai ya sanar, wannan tsarin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Disamba kuma an yi shi ne domin cimma wasu manyan manufofi A cewar gwamnan, baya da malaman makaranta da ma’aikatan asibiti, ranar Juma’a ma’aikata za su kasance a gida inda za su yi aikinsu ta yanar gizo.

 

 

 

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sabon tsarin kwanakin aikin gwamnati a fadin jihar Kaduna.

 

 

 

Kamar yadda gwamnan ya sanar a shafinsa na Facebook, za a fara wannan sabon salon ne zuwa ranar 1 ga watan Disamban wannan shekarar.

A cewar gwamnan:

 

 

“Gwamnatin jihar Kaduna za ta fara sabon sauyin aikin kwanaki hudu a mako a jihar. Na wucin-gadi, za a bar ma’aikatan gwamnati su dinga aikin kwana daya daga gida.

 

 

“An tsara wannan ne domin taimakawa wurin habaka yawan aiki, kawo inganci tsakanin rayuwar ma’aikaci da aikinsa tare da bai wa ma’aikata damar samun lokaci da iyali, hutawa da kuma noma.

 

“An dauka wannan matakin ne sakamakon darasin da aka koya daga annobar korona wanda ke bukatar sakin tsoffin tsarikan aiki tare da rungumar aiki ta yanar gizo kuma daga gida.”

 

 

Kamar yadda takardar da ta fito daga gidan gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana, za a fara wannan tsarin ne daga ranar daya ga watan Disamban wannan shekarar.

 

 

 

Daga wannan ranar, an sauya sa’o’in aikin ma’aikatan gwamnati inda zai koma daga karfe takwas na safe zuwa karfe biyar na yammaci, Litinin zuwa Juma’a.

 

 

 

Dukkan ma’aikatan gwamnati baya da malaman makaranta da masu aikin asibiti, za su dinga aiki daga gida a ranakun Juma’a. Wannan tsarin aikin zai cigaba har zuwa lokacin da gwamnati ta shirya zuwa matakin gaba na sauyin a jihar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “El-Rufai ya sauya tsarin aikin gwamnatin Kaduna, za a koma aikin kwana 4 a mako”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *