• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

EFCC TA CAFKE ROCHAS OKOROCHA

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha bayan sa’o’i su na mamaye da gidan sa a Maitama Abuja.
Okorocha wanda ke cikin ‘yan takarar shugaban kasa a APC ya shaidawa manema labaru cewa an shirya makircin hana shi samun shiga tantance ‘yan takara ne.
Okorocha ya taba fadar cewa EFCC ba ta taba barin sa ya sarara ba tun saukar sa daga kujerar gwamna.
Jami’an tsaro sun jefa borkonon tsohuwa don tarwatsa magoya bayan Okorocha inda daga bisani a ka yi awun gaba da shi cikin mota Hilux

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “EFCC TA CAFKE ROCHAS OKOROCHA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.