• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

EFCC: AN NADA GEORGE EKPUNGU A MATSAYIN SAKATAREN MAJALISAR KULA DA HUKUMAR EFCC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada George Ekpungu daga jihar Kuros Ribas a matsayin sakataren majalisar kula da hukumar yaki da cin hanci EFCC.
Nadin na kunshe ne a wasika da shugaban ya aikawa majalisar da shugaban majalisar Ahmed Lawan ya karanta.
Membobin hukumar sun hada da Luqman Muhammed daga Edo, Anunba Adaeze daga Enugu, Kola Adeshina daga Kwara da Yahaya Muhammed daga Yobe.
A wasikar shugaban ya ce tanadin dokar hukumar ta EFCC ya sanya shi aika sunayen don amincewa da su, kuma ya na fatar majalisar za ta amince da su a takadirin lokaci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *