• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ECOWAS TA DAU TSAURARAN MATAKAI KAN GWAMNATIN SOJA TA MALI

Kungiyar raya tattalin arzikin Afurka ta yamma ECOWAS ta dau tsauraran matakai kan gwamnatin mulkin soja ta Mali don yanda ta zake da neman makalewa kan mulki.
Biyo bayan juyin mulkin da sojojin su ka yi a 2020, a yanzu sun fito da tsarin maida mulki hannun farar hula har tsawon kimanin shekaru 5 nan gaba.
Sojojin dai sun tilasta tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ya yi murabus inda daga nan su ka share fagen mulkin soja.
Matakan ECOWAS sun hada da rufe kan iyakar sama da kasa wajen hana Mali hulda da sauran kasashen Afurka ta yamma, janye jakadu da ma rike duk kadarorin kasar da ke sauran kasashen kungiyar.
ECOWAS ta gudanar da taron ne a Accra Ghna a farkon makwan nan.
Bayanan taron na kunshe ne a sanarwa daga mai taimakawa mataimakin shugaban Najeriya kan labaru Yemi Osinbajo wato Laolu Akande wacce ta ce Osinbajo ya wakilci shugaba Buhari a wajen taron.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ECOWAS TA DAU TSAURARAN MATAKAI KAN GWAMNATIN SOJA TA MALI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.