• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DUSAR KANKARA TA YI SANADIYYAR MUTUWAR MUTUM 21 A PAKISTAN

ByNoblen

Jan 9, 2022

Tsananin dasar kankara ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 21 a kasar Pakistan yayin da su ka makale a cikin motocin su.
Ba tabbaci dukkan mutanen sun mutu ne a motocin su ba ya ga 6 da a ka samu a motocin, inda a ke ganin tururin da ya samu daga kankarar ya yi sanadiyyar mutuwar sauran mutanen.
Akasin ya auku ne a yayin da dubban mutane su ka yi dafifi don ganin dusar kankara a gari mai tsaunka da kankarar kan taru ba.
Yawan motocin ya sa mutane su ka makale a waje daya inda dusar kankarar ta yi tudu a kan motocin sun a tsawon mita daya.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Sheikh Shahid ya ce an tura sojoji don share hanya da ceto dubban mutane da su ka makale a kusa da yankin na Murree da ke tazarar kilomita 70 a arewa maso gabashi daga babban birnin kasar Islamabad.
Firaministan kasar Imran Khan ya nuna matukar kaduwa ga aukuwar akasin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *