• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DUNIYAR HAUSA TA YI RASHIN BATURE MAI MAGANA DA HAUSA FILLA-FILLA MR.STEVE LUCAS

Duniyar Hausa ta yi rashin bature da ke magana da Hausa tamkar bahaushe Mr.Steve Lucas, wanda ya riga mu gidan gaskiya a Florida ta Amurka bayan gajeruwar jinya.
Sanarwa daga shugaban sashen Hausa na Muryar Amurka a Washington DC Aliyu Mustapha Sokoto ta nuna juyayin rasuwar Mr.Lucas wanda tsohon shugaban sashen na Huasa ne kuma tsohon shugaban sashen Afurka na VOA kazalika kafin ritayar sa ya zama shugaban sashen kula da rediyoyi na duniya na VOA.
Mr.Lucas wanda a ka haifa a Filato ta Najeriya ya yi ritaya daga aikin Muryar Amurka bayan shekaru 25 inda daga nan ya koma jamhuriyar Nijar da zama shi da matar sa Fatima wacce ‘yar Nijar din ne.
Mr.Lucas ya yi rangadi inda ya gana da manyan masu sauraron Muryar Amurka musamman a Najeriya, Nijar da Ghana.
Mutane na ta aika sakonnin juyayin rasuwar marigayin da kan karanta labaru da murya mai dadin gaske dalla-dalla.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DUNIYAR HAUSA TA YI RASHIN BATURE MAI MAGANA DA HAUSA FILLA-FILLA MR.STEVE LUCAS”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *