Bayan zaben kananan hukumomi da kansiloli a jihar Nassarawa Najeriya, shugaban majalisar sarakuna na jihar Alhaji Sidi Bage na daya ya ce za su zuba ido kan zababbun don tabbatar da sun cika alkawuran kamfen.
Sarakuna dai da a ka saba jin su na kira kan zaman lafiya, ba sa tsanantawa don rashin tanadin tsarin mulki da ya ba su irin wannan karfi.
Bage ya ce duk shugaban karamar hukumar da ya gaza cika alkawarin kamfen za a sauke shi kuma a sake sabon zabe.
Basaraken ya ce ba za a zuba ido a bar wasu shugabannin kananan hukumomi ko sauran zababbu ba sa zuwa aiki sai lokacin Kason kudi ba.
Sarkin ya bukaci jama’a su tsaya kan hakkin su don ya zama shugabannin da a ka zaba sun sauke nauyin da su ka dorawa kan su.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Thanks for the good article, I hope you continue to work as well.