• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DUK JAMI’AN GWAMNATIN DA KE DA NIYYAR TAKARAR MUKAMAI SU YI MURABUS-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara fitowa filla-filla inda ya umurci duk masu rike da mukamai a gwamnatin sa kama daga ministoci, jakadu da ma gwamnan babban bankin Najeriya CBN da ke da sha’awar takarar mukamai a zaben 2023 su yi murabus.

A wasika ga jami’an daga sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha shugaban ya umurci duk wadanda lamarin ya shafa su mika wasikar su ta murabus gabanin ranar litinin 16 ga watan nan na mayu.

Hakan ya biyo bayan taron majalisar zartarwa na mako inda a ka fitar da a ka dau matakin don lura da yanda wasu jami’ai su ke cikin gwamnatin alhali su yi ta zirga-zirgar neman takarar zabe.

Ga ministocin da ke son murabus su mika ragamar ma’aikatu ga kananan ministoci ko in ba karamin minister su mika ga manyan sakatarori.

Su ma jakadau sais u mika ofis ga mataimakan su ko manyan jami’ai a ofishin jakadancin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DUK JAMI’AN GWAMNATIN DA KE DA NIYYAR TAKARAR MUKAMAI SU YI MURABUS-SHUGABA BUHARI”
 1. Hi there

  I wanted to reach out and let you know about our new dog harness. It’s really easy to put on and take off – in just 2 seconds – and it’s personalized for each dog.
  Plus, we offer a lifetime warranty so you can be sure your pet is always safe and stylish.

  We’ve had a lot of success with it so far and I think your dog would love it.

  Get yours today with 50% OFF: https://caredogbest.com

  FREE Shipping – TODAY ONLY!

  To your success,

  Susanna

Leave a Reply

Your email address will not be published.